BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Tambayoyi Da Amsar su tare da
Sheikh Ibraheem Zakzaky na Arba'in da biyu
Mai karatu yau ma muna dauke maku ne da wasu daga cikin tambayoyinku, da amsoshinsu, wadanda muka samo kai tsaye daga Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky mai albarka. Muna kara yin kira ga al’ummar musulmi da su rinka aiko mana da tambayoyinsu game da abin da.........
Mai karatu yau ma muna dauke maku ne da wasu daga cikin tambayoyinku, da amsoshinsu, wadanda muka samo kai tsaye daga Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky mai albarka.
Muna kara yin kira ga al’ummar musulmi da su rinka aiko mana da tambayoyinsu game da abin da ya shige masu duhu a cikin addinin Musulunci. Amma muna so a aiko mana da tambayoyi masu ma’ana. Kuma a rinka lura da kyau kada a rinka maimaita tambaya.
Sannan kuma muna kira ga dimbin masu shirin aiko mana da tambayoyin su da cewa akwai bukatar a rinka yin hakuri, za mu yi kokari mu bi layi wajen mika tambayoyin ga Sayyid. Don haka in Allah ya yarda, in dai tambayar mutum tana da ma’ana, to komai dadewa zai ga amsa a wannan fili. Za a iya aiko da tambayoyin ta wadannan hanyoyi, imel: almizanzariya@yahoo.com, almizan80@hotmal.com. Ko kuma ta wayar salula, 0803 451 4631.
Musa Muhammad Awwal ya rubuto mana. Tare da fatan Allah ya kara wa Sayyid lafiya da kariya ta musamman daga dukkan sharri. Mu kuma Allah kara mana biyayya da fahimtar abin da Sayyid ke nusar da mu.
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, kusan a kowane lokaci idan ina salla ni kadai sai na samu shakku a cikin sallata, kuma na fi samun shakka a wajen zaman tahiya na farko. Malam me ya kamace ni?
Daga Musa Dan Alhaji Kaduna
AMSA: To, mai yawan shakka, yana mantawa da shakkan ne. Zai dauka sallarsa ta yi daidai, ya manta da shakka. Don in na fahimce shi, shi mai yawan shakku ne, shi kuwa mai yawan shakku yana mantawa da shakkar ne, musamman in ya zama duk salla sai ya yi shakka, to shi kenan sai ya manta da shakkar kawai.
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, ni ne ina salla, na manta ban yi tahiya ta farko ba, kuma ban tuna ba sai da na mike na fara karatu. Me ya kamata in yi a wannan lokaci?
Daga Musa Dan Alhaji Kaduna
AMSA: Zai ci gaba da salla ne, sai in ya sallame sai ya rama zama na farko. Zama na farko da sujada daya in an tsallake su, ana biyan su a wajen salla, ana kada’insu. Amma banda wadannan ba wanda ake yin su a wajen salla. Wato bayan ya sallame sai kuma ya sake yin tashahhud, a na tsakiya din kenan da bai yi ba.
TAMBAYA: Akramakallahu, ni ne zan yi tafiya, amma ban bar garinmu ba sai da zawwal na lokacin salla ya shiga, amma farkon shigar lokacin ne na bar gari, misali karfe 1 na rana. Shin in na je tafiyar nan, kasaru zan yi ko, kuwa duk zan yi ihtiyadan?
AMSA: To, ashe shi kansa ma ya san amsa din kenan. Tunda cika salla ya kama shi yana gida, to lallai ko ya yi tafiya din cika salla zai yi, kuma sai ya yi kasaru, Ihtiyadan. Haka zalika ma, abin da bai tambaya ba, in zai dawo gida, to idan lokacin salla ya same shi yana kan tafiya, sai ya iso gida bai yi sallar ba, idan yana nan a lokacin, to zai cika salla ne, sai ya yi kasaru ihtiyadan. Amma shi ihtiyadan na farko ya fi karfi. Lallai shi wannan duka sallolin biyu sun hau kansa, sabanin na dawowa gida, in dai lokacin salla bai fita ba, in ya cika shi kenan, ihtiyadan, bai zama lazim ba.
TAMBAYA: Allah ya kara wa Malam lafiya da kariya. Na wayi gari da azumi, saboda wani dan uwa ya ce an ga wata. Amma sai na ji a BBC an ce sai gobe ne za a dauki azumi, sai na ci abinci. Daga bisani kuma sai Maigidana ya ce lallai duk ’yan uwa suna azumi. Me ya hau kai na?
Daga A’isha
AMSA: To, in dai kamar bayanin da ya yi, shi ya dauka an ga wata, sai kuma ya dawo ya dauka ba a gani ba, sannan sai ya dawo ya tabbatar cewa an gani, saboda haka ya ci abinci da tsammanin ran nan ba Ramadan ba kenan. Saboda haka yanzu abin da ya hau kansa kawai shi ne ya yi ramuwa.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam mutum ne Mai gidansa ba ya ba shi hakkinsa yadda ya dace, amma shi yaron idan an tashi sai ya rinka daukar wani abu, alhali shi Mai gidan bai sani ba. Ya wannan abin yake?
AMSA: Lallai abin da ya dauka, tunda ba hakkinsa ba ne, to duk cikarsu sun zalunci juna kenan. Maigidansa ya zalunce shi ya kin ba shi hakkinsa, shi kuma ya zalunce shi ya yi masa sata.
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, ko zan iya wanke bakina da makilin da rana a lokacin azumi?
Daga Yahaya Garba Gwamna Bunkure
AMSA: Mun sha amsa irin wannan tambayar. Yana iya wankewa matukar dai ba zai hadiye ba. Wadansu sukan ce yana da dandano, to dandanon abu, in dai ba ya wuce makoshi ba ne, ba komai. In dai ya dandana ya furzar. Saboda haka ba laifi da wanke baki da shi, ko da kuwa yana da dandano.
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, ni dai mutum ne mai rauni a ibada. Ina barar addu’a da kuma shawarar da zan bi don inganta kwazo a ibada?
Daga Abubakar Umar Niamey
AMSA: Masha Allah, ina fata raunin nasa a nafiloli ne, ba a farali ba. In a nafiloli ne, akwai a cikin ‘misbahul Mutahajjid’, ya kawo shawarwarin yadda wanda ke sake da sallar dare zai yi idan yana sake da sallar dare, akwai wasu surori da zai karanta. Yanzu ba zan kawo su ba, amma ya duba littafin zai gani. Amma ina fata na nafila ne, ba yana sake da farali ba ne.
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, ko zan iya daukar wacce zan aura a mashin, duk da kuwa ba a daura auren ba?
AMSA: To, dai wadda zai aura bai dai aure ta ba. Saboda haka muharramarsa ce. In abin da yake nufi shi ne jikinsu zai hadu, yana ganin tun da zai aure ta, sai mu ce masa a’a, tana nan a muharramarsa har sai an daura masu aure.
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, wasannin tashe da ake yi idan azumi ya kai kwana goma, menene asalinsa, kuma ya matsayinsa a Musulunci?
AMSA: Al’ada ce dai kawai. Kuma abin mamaki kusan ko’ina a kasashen musulmi suna wannan al’ada din, yakan bambanta tsakanin wannan wuri da wannan wuri, kasashen Larabawa suna yi, wasu wurare ya zama zaunennan abu, mai yiwuwa saboda yanayin rayuwa irin ta da mutanen da, da duhu, da kuma sai an ta da mutane. Amma kuma yanzu ya zama kawai wasannin ne, ba a bukatar sa. Amma a da ana bukatar sa sosai don a tashi mutane su dafa abinci, amma yanzu ba a bukata, saboda mutane suna da agogwanni masu karaurawa, da kuma yanzu ma daren ma ba a cika barci sosai ba. Amma dai al’adar mutane ne, kuma ba laifi da shi, tun da ba an ce aibada ne da aka ruwaito ana yi ba. Al’ada ce kuma ba ta yi karo da shari’a ba, saboda haka ba komai. Allahumma sai dai in akwai wasu abubuwa da ake yi a tashen, wanda ya saba ma shari’a, sai a ce to su a bar su. Amma shi tashe a kashin kansa kawai al’adar mutane ne.
TAMBAYA: Allah gafarta ya Malam ko zan iya karatun Kur’ani a cikin sujada a sallar nafila?
Daga Abdurrashid Na’ibawa Kano
AMSA: A’a, ba a karanta Alkur’ani a ruku’u da sujuda, sai dai in wani bangare nasa da ya bullo da unwanin addu’a, kamar ‘rabbana atina fiddunya hasana’, ko abin da ya yi kama da haka nan, amma ba matsayin kira’a ba. Kira’a a tsaye ake yi, amma ba a yi a sauran wurare.
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, an ce balagar ’ya mace shekara 10, namiji kuma shekara 14. Tambayata ita ce, ‘ya ta shekararta 10, amma kuma azumi na ba ta wahala, ita da dan uwanta. Shin Malam me ya kamata in yi?
Daga Ibrahim Adam Dunburde
AMSA: To, na farko dai ba a ce shekara 10 ba ne, 9 ne ma, bai kai 10 ba, ga ’ya mace. Shi kuma namiji yakan zama galiban 12 ne. Yanzu muna ganin abubuwa na sassakewa na yanayin jikkunan yara din, wala’alla shi ya zo a rubuce haka nan. Don da mu mun saba yara din ba sukan balaga ba, kamar maza, sukan kai 17 a da can, mata kuma sukan kai 14, amma sai muka ga yanzu balagar tasu tana komowa baya, wala’alla shi ya sa shari’a ta zo da shi don ta san zai kai haka nan. To, idan yarinya ba za ta iya azumi ba, to sai a dauki wadansu matakin da za a iya saukaka mata, kamar misali a kirkiri tafiya. Amma dai lallai matukar tana nan, azumin ya hau kanta. Sai dai ni ina ganin wannan rashin iyawar, kila har da rashin tarbiyyantar da yaran su yi azumi tunda wuri. Tunda mu yaranmu nan, ba su shan azumin tun kasa da shekara 7, suna Ramadan din su cikakke, kuma har su kai balaga din. Amma lallai in har ba za ta iya ba, to lallai kuma ya hau kanta. Saboda haka sai dai a bi wata hanya ta shari’a, alal misali tafiya. Sai a kirkiri tafiyar da zai ja mata ta sha, har a jira in kafin wani Ramadan za ta yi azumi, sai ta rama.
TAMBAYA: Mutum ne ya wayi gari da janaba a watan Ramadan. Ina matsayin azuminsa na wannan rana?
Daga Salmanu Bakori
AMSA: To, idan ba bisa sakensa ne ya sa ya kwana da janabar ba, kamar alal misali, barci ne ya rinjaye shi, sai gab da ketowar alfijir sai ya yi mafarki, misali. Amma banda kamar a ce shi ya sabbaba ma kansa janaba din, kamar ta hanyar saduwa da iyali, sai ya ga dama ya kwanta kafin alfijir, sai alfijir ya keto, ka ga wannan da gangan kenan. Wato wannan tambayar da yake yi, za mu iya cewa kamar ba shi ne ya sabbaba ma kansa ba, tunda shi bai gaya mana yadda janabar ta samu ba. In ba shi ne ya yi sake ba, ya zama gari ya waye masa da janaba din ba, to sai ya zama ramuwar wannan azumin ne kawai ya hau kansa. In da sake a nasa bangaren. Alal misali ya san da janabar, ya wayi gari da ita, ko ya yi gangancin yin barci gab da ketowar alfijir, to lallai ramuwa da kaffara ne a kansa.